Karatu a kasar Brunei (Darussalam)
Ma’aikatara kula da harkokin wajen kasar Brunei na farin cikin sanar da daukacin daliban kasashen ketare tare da gayyatar su zuwa cika scholarship ta kasar na shekarar 2022/2023.
Kasar Brunei (Darussalam) suna bada karatu kyauta (scholarship) kama daga kan karatun diploma,undergraduate degree,master degree da Ph. D.
Ga wasu daga cikin makarantun kasar Brunei (Darussalam) wadanda zasu bada scholarship a wannan shekarar da muke ciki,kuma sun bude shafinsu na yanar gizo yanzu haka ga wadanda suke san cikawa. Gasu kamar haka:
• Universiti Brunei Darussalam (UBD)
• Kolej Universiti Perguruan Ugama Seri Begawan ( KUPU SB)
• Universiti Islam Sultan Sharif Ali (UNISSA)
• Universiti Teknologi Brunei (UTB)
• Politeknik Brunei (TB)
A takaice:
• Kasa: Government of Brunei
• Yankin karatu: Yankin Asia
• Nau’in karatu: Undergraduate scholarship,Postgraduate scholarship da Masters scholarship
• Kasashen da suka cancanta: Dukkan kasashe
• Rewards: Biyan cikakken kudin karatu
• Lokacin rufewa: February,15/2022
Karin bayani
Makarantun kasar ta Brunei suna da tsare tsare na karatu kama daga kan jadawalin kwasa kwasan da suke yi zuwa abubuwan da ake da bukata yayin cika wannan scholarship din,karin bayani akan haka kuma za’a iya samun sa a daya daga cikin wadannan shafukan nasu;
• Universiti Brunei Darussalam -
• Universiti Islam Sultan Sharif -
• Universiti Teknologi Brunei -
• Politeknik Brunei - www.pb.edu.bn
Abubuwan da ake bukata
Ita wannan scholarship ana bada tane ga ’yan asalin kasashen ketare ma’ana ba kadai sai ’yan kasar ta Brunei ba,shine bata tsaya kadai ga kasashen da suke karkashin hadakar ASEAN (Association Of Southeast Asian Nations) ba,kowace kasa zata iya neman wannan scholarship din.
Sannan yayin cika wannan scholarship dole dalibi ya zama tsakanin shekara sha takwas zuwa shekara ashirin da biyar (18-25) a bangaren masu karatun diploma ko digiri kenan,a bangaren masu karatun masters da Ph D kuma kada mutum ya wuce shekaru talatin da biyar (35).
Har wayau dai wannan scholarship bata sahhalewa mazaunin cikin kasar ta Brunei Darussalam ba,sai dai wadda yaje kasar ta hanyar kasuwanci ko kuma zama wadda yake bana din din din ba.
Abubuwan da dalibai zasu amfana da wannan scholarship din
Ga kadan daga cikin abubuwan da daliban da suka samu wannan scholarship din zasu samu;
• Dalibi zai biya wasu daga cikin kudaden makaranta da suka hada da tuition fee,acceptance,examination,registration da kuma orientation fee a lokacin fara karatun su kuma zasu biya sauran daga bisani.
• Biyan kudin jirgi (Air-tickets) daga kasar da dalibi yake zuwa kasar Brunei Darussalam,da kuma biyan kudin jirgin yayin kammala karatu zuwa kasar ka.
• Biyan alawus kowane wata na kimanin dala dari da hamsin $150.00
• Biyan kudin makulashe duk karshen wata shima dala dari da hamsin $150.00
• Biyan kudin littafi duk karshen shekara daya kai dala dari shida $600.00
• Akwai wadataccen wurin kwanan dalibai acikin makarantar da kuma isashshen tsaro
Sauran abubuwan da ake da bukata
Ana bukatar dalibi daya;
• Tabbatar daya bi dukkan sharudan wannan scholarship din
• Tabbatar da bin dokokin makarantar daya samu jami’a ko polytechnic
• Kiyaye ka’idojin kasar da kuma da’a wajen zamantakewa,al’adu da addinin kasar Brunei Darussalam
• Barin shiga harkokin siyasa
• Tabbatar da gwajin lafiya daga hukumar kasar Brunei Darussalam
• Bayan kammala karatu ana umartar dalibi da barin kasar da zarar ya kammala
Yadda za’a cika wannan scholarship
Za’a iya cika wannan scholarship din ta hanyar sauke application form din:
http://www.mfa.gov.bn/PublishingImages/Pages/bdgs/bdgs2022/BDGS%20APPLICATION%20FORM%202022-2023.doc
Dole wannan form a cika shi dai dai sannan a tura shi zuwa ma’aikatar kula da harkokin kasar da dalibin yake ko kuma zuwa National Focal Point na kasar da dalibin yake
Ana da bukatar dalibi daya mika bayanan tabbacin rashin samunsa da aikata laifuka daga hukumar tsaron kasa ta National security agency/Police station cewar ba’a taba samunsa da aikata laifi ba
Bayan an harhada bayanan sai a tura su ta wannan email address din:
(Abin lura anan shine duka girman takardun da sauran files basu wuce megabyte goma ba 10MB)
Kuma dai alura da cewar duk form din da za’a tura ya zama ta hanyar document format ne ma’ana / PDF/ JPG format (compressed (.zip) folder)
Sannan dalibi zai kammala cika form dinsa online ta wannan link din:
Duk application din daya zama incomplete to baza a karbeshiba
Ana kuma bukatar dalibi daya bayyana lokacin ganawar baki da baki (interview) a wurin da aka sanar domin tabbatar da ingancin yaren dalibi na turanci,larabci da malay
Kadai ga daliban da suka samu ne za’a sanar dasu ta email address nasu.
Ga link din👉http://www.mfa.gov.bn/Pages/bdgs/bdgs2022.aspx