A yau wannan shafin zai kawo muku wasu hanyoyi daza kubi domin dawo da account dinku na facebook idan masu kutse sun sace shi.Zaku iya wannan ta hanyar canza lambobin sirri ma’ana “password” ko kuma ta hanyar tura report wa kamfanin na facebook a matsayin bada izininka aka shiga maka account dinka ba.
Ga wasu daga cikin matakan da zaku bi domin magance wannan matsalar da ikon Allah.
1. Mataki na farko shine “Resetting your password on mobile”
Da farko zaka bude facebook app dinka,shine wani me kalar shudin duhu da farar alamar fa “f” akansa.Wannan zai kaika zuwa wurin saka bayanan ka idan an kwace maka account din kenan.
2. Na biyu zaka zaka danna “Need help”.Shi wannan link din yana kasa da wurin saka adireshin email da wurin saka password,wani rubutu zai bayyana inda aka rubuta;
• Forgot Password?
3. Saika danna “Forgot Password” da zarar ka danna zai kaika zuwa shafin da zaka canja password dinka.
4. Zaka saka email address dinka ko lambar waya,saika danna wurin rubutu a saman shafin da kake,saika rubuta adireshinka na email ko kuma lambar wayar da kake amfani da ita wajen bude facebook account dinka.
• Idan kuma baka taba saka/ko kara lambar waya a facebook dinka ba,to sai kayi amfani da adireshinka na email.
5. Sai ka danna “Search” wani shudin rubutu a kasan wurin da kayi rubutun.Wannan zai kawo maka account dinka na facebook.
6. Sai ka danna “account recovery method” ,wannan zai baka zabi guda biyu,ma’ana tayaya kake son sakon yazo maka shin;
• ta hanyar email kake so - facebook zai turo maka wasu lambobi ta email din daka bude facebook account dinka,ko kuma;
• ta hanyar sakon waya ma’ana SMS - facebook zai tura maka da sakon text na wasu lambobi ta layin dakayi rigistar facebook account dinka.
7. Saika danna “Continue” shima wata alama ce me kalar dark-blue a kasa da account recovery options.Yin haka zaisa facebook su turo maka lambobin ta email ko text.
8. Retrieve your account’s code.
Bayan facebook sun turo maka da lambobin (code),amma ya danganta da wace hanya ka karbi sakon,idan ta email ne saika shiga akwatin email dinka domin daukar lambobin ko kuma ta hanyar sakon waya(text) shima saika shiga message domin daukar lambobin.Lambobin dai guda shida ne facebook yake turawa,kuma sunan sakon ma na facebook din ne.
9. “Enter the code”. Saika danna wurin da zaka saka lambobin kamar haka “Enter your six-digit code” a wurin da zaka rubuta,saika rubuta wannan lambobin guda shida da facebook suka turo maka ta hanyar email ko text.
• Ka tabbatar baka yi jinkirin saka lambobin ba saboda zasu yi expire idan suka kai adadin wasu dakiku baka sanya suba.
• Amma zaka iya danna alamar “Resend Code Option” domin sake turo maka wani sabon code din.
10. Saika danna alamar “Continue” yin hakan zai kaika zuwaga wani shafin.
11. Saika duba akwatin da aka rubuta “Log me out of other devices” saika danna alamar “Continue” da zarar kayi haka duk inda aka saka account dinka na facebook kodai akan kwamfuta (computer),tablet ko kuma wayar hannu (android phone) da aka dora account dinka to zaiyi logging out da kansa koda kuwa shi hacker din bai isa ya dakatar da hakan ba.
12. Bayan haka saika saka sabuwar password(ba irin waccan ta farko da akayi maka kutse da ita ba) saika danna “Enter a new password” zaka saka sabuwar password a cikin akwatin rubutu yananan akusa da saman shafin.
13. Saika danna “Continue” wannan na nufin ka musanya tsohuwar password dinka da sabuwa.A yanzu kuma zaka iya shiga account dinka na facebook da sabuwar password dinka,sannan shi wadda ya kwace maka account din bashi da damar sake shiga ciki,kayi maganinsa ensha Allah.
☆ Mataki na biyu shine zaka turawa kamfanin facebook report shine “Reporting the hacked account to facebook”
1. Zaka bude shafin da aka kwace maka account din.Saika tafi zuwa
https://www.facebook.com/hacked/ akan browser na kwamfutar ka.
2. Saika danna wurin da aka rubuta “My Account is Compromised”. Shima wani shudin guri ne a tsakiyar shafin,yin hakan zai bude maka shafin searching.
3. Saika shiga email address dinka ko lambar waya.Zaka danna wurin rubutu ne shima a tsakiyar shafin,saika saka email address dinka ko lambar wayar dakayi rigista da ita wadda kake sakawa yayin shiga facebook dinka.
• Idan baka taba kara lambar waya a facebook account dinka ba,to sai dai kayi amfani da email address dinka.
4. Saika danna alamar “Search” wadda ke dama da wurin rubutu ma’ana text field,wannan zaisa facebook su shiga neman account dinka.
5. Saika danna “Enter a password” zaka saka password din da zaka iya tunawa na account dinka,zakayi haka ne a wurin “Current or Old Password” text field.
6. Ka danna “Continue” shima wani shudin alamane a kusa da karshen shafin.
7. Da zarar ya bude maka shafin zasu
tambayeka ka zabi dalilin dayasa aka kwace maka account kamar haka;
• I saw a post,message or event on my account that I did’nt create
• Someone else got into my account without my permission
• I don’t see the right option on this list
Zaka zabi daya daga cikin wadannan dalilan,ya danganta da yadda ake maka posting a account din naka.
8. Saika danna “Continue” wannan zai kaika zuwa farkon shafin da aka kwace maka account din.
• Idan ka duba daya daga cikin options din ba’a lissafo dashi a cikin “Valid reason” ba a baya to zaka kare ne a shafin kulawa na facebook ma’ana facebook help page.
9. Saika danna “Get started” wadda ke kasa dama da gefen shafin.Yin hakan zai baiwa facebook damar canza ayyukan da kayi.
10. Saika danna alamar Continue wadda ke kasa dama da gefen shafin.
11. Saika saka sabuwar password duka a wuraren da suka rubuta “New text field”da kuma wurin “Re- type New” text field.
12. Saika danna “Next” shima shudin rubutu ne a kasa da shafin.
13. Saika duba akwatin dayake kusa da sunan ka,saika danna “Next” yin hakan zaisa a dauki sunan ka a matsayin sunan account dinka.
• Amma idan baka san wanna zabin zaka iya tsallakeshi zuwa mataki na gaba.
14. Saika shiga wurin da aka rubuta “Edit my information that you did’nt change’ facebook zasu bayyana maka posting mabanbanta masu yawa da saiti(setting) da sauran canje canje aka gudanar,zaka iya amsar wadannan saituna idan har kaine kayi su,koka ki amsarsu koma ka goge su idan wani ne daban yayi maka su batare da saninka ba.
• Idan kuma sun kaika zuwa wurin gyara posting din da kayi zaka iya tsallakeshi ka tafi zuwa wani shafin.
15. Saika danna “Go to News Feed” wannan zai kaika zuwa wurin labaranka na facebook.Yanzu kana da cikakkiyar damar amfani da facebook dinka ensha Allah.